26 Agusta 2020 - 13:06
Tattaunawar Iran Da Hukumar (IAEA) Ta Yi Matukar Armashi

Iran, ta ce tattaunawar da ta yi da shugaban hukumar yana yaduwar makamman nukiliya ta duniya wanda ke ziyara a kasar ta yi armashi.

ABNA24 : Da ya ke sanar da hakan ga manema labarai shugaban hukumar makamanshin nukiliya ta Iran, Ali Akbar Salehi, ya ce tattaunawar da sukayi da shugaban hukumar ta (IAEA), Rafael Mariano Grossi, yau Talata ta yi armashi sosai.

Yayin tattaunawar bangarorin biyu sun amince hukumar ta IAEA, ta ci gaba da aikinta a kasar ta Iran ba tare da nuna bangaranci ba, kamar yadda Mista Salehi din ya shaidawa kamfanin dilancin labaren IRNA.

Ziyarar ta Rafael Grossi, wacce ita ce irinta ta farko a Iran, tun bayan da ya kama shugabancin hukumar ta IAEA, zata bude wani sabon babi tsakanin Iran, da hukumar musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar takun-tsaka tsakanin Amurka da Iran da sauren mayan kasashen duniya game da bukatar Amurka na neman tsawaita takunkumin cinikin makamai ga kasar ta Iran.

342/